ABNA24 : Har ila yau Mahadi Mir Ashrafi ya kara da cewa; Kasar Sin ce a gaba da sayan hajar ta Iran da ta kai ton miliyan 4.6 bisa kudi dalar Amurka biliyan 2, sai kuma kasashen Iraki da hajar da ta saya ta kai ton miliyan 3.1,da kudin da su ka kai dalar Amurka miliyan 953.
Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa kuwa ta sayi hajar ta Iran ne da ta kai ton miliyan 2.4 da kudi dalar Amurka miliyan 2.4. Daga nan kuma sai Turkiya da sayi hajar da ta kai ton dubu dari 384 akan dalar Amurka miliyan 388, sai Afghanistan da ta sayi hajar da ta kai ton 911 da kudi dalar Amurka miliyan 365.
342/